Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

PDP Ta Tsayar Da Goodluck Jonathan


Goodluck Jonathan yana jawavi ga wakilai a taron PDP na tsayar da dan takarar shugaban kasa a Abuja.

Shugaba Jonathan ya kada tsohon mataimakin shugaba Atiku Abubakar da kuma Sarah Jibril ya zamo dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar mai mulkin Najeriya

Jam'iyyar PDP mai mulkin Najeriya ta zabi shugaba Goodluck Jonathan domin ya zamo dan takararta a zaben shugaban kasa da za a yi cikin watan Afrilu.

Mr. Jonathan ya samu kuri'u dubu biyu da dari bakwai da talatin da shida (2,736) yayin da babban mai hamayya da shi, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ya samu kuri'u dari takwas da biyar (805). Sarah Jibril ta samu kuri'a kwaya daya tak.

A yau jumma'a, Mr. Jonathan ya karbi garkuwar yakin ta jam'iyyar PDP yana mai rokon Atiku Abubakar da Sarah Jibril da su yi aiki tare da shi wajen habaka Najeriya. Yace wannan lokaci ne da ya kamata kasar ta hada kai.

Atiku Abubakar, wanda Musulmi ne daga arewacin Najeriya, ya soki Mr. Jonathan, Kirista daga kudu, a saboda karya haddin tsarin jam'iyyar na karba-karba kan kujerar shugaban kasa.Jam'iyyar PDP tana karba-karba a tsakanin kudanci da arewacin Najeriya a bayan wa'adi bibbiyu.

Mr. Jonathan ya zamo shugaban kasa a watan Mayu na bara, lokacin da Umaru Musa 'Yar'aduwa, Musulmi daga arewa, ya mutu a cikin shekara ta uku ta shugabancin da aka tsammaci zai yi na tsawon shekaru takwas. Wasu 'yan jam'iyyar sun so a tsayar da wani dan arewa domin yin takarar wannan kujera.

XS
SM
MD
LG