Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomi Na Ci Gaba Da Takun Saka Da Masu Zanga Zanga A Hong kong


Masu zanga-zangar goyon bayan dimokaradiyya, da dayawan su dalibai ne, sun killace kan su a jami’o’i a Hong Kong, a dai dai lokacin da makarantun suka kasance wurare na baya-bayan nan da masu zanga-zangar ke bukatar ‘yancin cin gashin kai daga China.

An ci gaba da samun arangama mai muni tsakanin hukumomi da masu zanga-zangar.

A wani yunkurin dakile zanga-zanga a tituna a wannan makon, ‘yan sanda sun shiga jami’ar kasar China da ke Hong Kong, da jami’ar fasaha da kere-kere da kuma jami’ar jihar Hon Kong, suna harba barkonon tsohuwa a cikin makarantun biyu na farko.

Lamarin ya haifar da arangama a makarantu da dama.

Babbar arangamar ta tashi ne a jami’ar kasa ta Hong Kong.

Bayan ‘yan sanda sun shiga ginin jami’ar suka kama dalibai da dama, wadanda daga bisani suka caje su da laifin ta da tarzoma. Ginin makarantar ya koma wani shingen sansani. Dalibai da tsofaffin dalibai, da ma wasu daliban daga wasu jami’o’i, sun mamaye gadar makarantar, inda suka kukkunna wuta, tare kuma da jefa bama-baman kwalba, domin kange ‘yan sanda daga shiga ginin.

‘Yan sandan kwantar da tarzoma sun janye a daren ranar Talata.

Ya zuwa yammacin Laraba, ‘yan sanda sun ce masu zanga-zangar suna ci gaba da mamaye ginin jami’ar.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG