Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomi Sun Hana Jirgin Muhammadu Buhari Sauka a Makurdi


Muhammadu Buhari.

A wasu Rahotanni daga Najeriya na cewa hukumomin kasar sun hana jirgin daya daga cikin masu takarar shugabancin kasar a jam’iyyar hamayya janar Mohammadu Buhari sauka a jihar Benue.

Wani jigon jam’iyyar hamayya ta APC Farouk Adamu Aliyu, ya tabbatar wa Sashen Hausa na Muryar Amurka faruwar wannan lamari, inda ya kara da bayanin cewar, duk inda dan takarar shugaban kasar wato ganal Muhammadu Buhari zaije to sai an kira an nemi umarni.

Jirginsa dai zai tashine daga port court an shirya zuwa Makurdi, da aka kira sai ma’aikatan dasuke aiki tashar saukar jiragen sama sukace to tun da shine zaizo, dole saisun tambayo daga sama, andai jirasu aka kuma sake tuntubarsu sai sukace ai daga sama ance kar’abari jirgin yazo.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:22 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG