Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Hajji Da Masu Zuwa Birnin Kudus Su Fara Neman Hanyoyin Dogaro Da Kai


Shugaban hukumar aikin hajji na Najeriya Barrister Abdullahi Mukhtar ne yayi wannan kira lokacinda ya karbi takwaran aikinsa na kirista wanda ya kai masa ziyara.

Da yake magana tunda farko babban sakataren hukumar masu aikin ibada na kiristoci, John Kennedy Okpera, yace ya gabatarwa gwamnatin tarayya bukatar neman rangwame a cancin kudi, kuma idan har ya sami haka, musulmi masu tafiya aikin hajji zasu amfana.

Mr. Kennedy Okpera, yace wadannan hukumomi biyu su suka fi aiki tare, kuma hadin kansu zai taimakawa Najeriya.

Da yake karin haske Rev. Yohanna Amos, yace suna son ganin zuwa aikin ibada da hajji da 'yan Najeriya suke yi ya zamnato makaranta wajen sauya halin 'yan Najeriya su kasance mutanen kwarai, fiyeda halinda suke ciki kamin su tafi gabas.

Rev Amos yace matsalar Najeriya ba rashin kudi bane, sai dai wadanda aka dankawa amana, sun kasance ba mutanen kwarai ba.

Da yake magana shugaban hukumar aikin hajji na Najeriya Barrsiter Mukhtar Abdullahi Mukhtar ya shawarci hukumomin biyu su fara lalubo hanyoyin da zasu zamo masu dogaro da kai, kamin gwamnati tace zata tsame hanu daga ayyukan hukumomin.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:00 0:00

Bidiyo

Shugaban Gwamnatin Rikon Kwarya A Mali Goita Ya Tsallake Rijiya Da Baya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Sanarwar Neman Afuwa daga Malam Abdujabbar Kabara
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:36 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Yi Tattaki Gida Bayan Ya Idar Da Sallar Eid El-Kabir a Daura
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:06 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Zauren VOA: Najeriya da Kaubalen 'Yan Aware - 005
please wait

No media source currently available

0:00 0:22:55 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Matsalar Tsangwamar Mata Masu Saka Abaya A Kanon Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG