Babban masanin alkaluma a Najeriya, Yemi Kale, ya fada ran Lahadi cewa ana kiyasin tattalin arzikin Najeriya ya kai kusan dala miliyan dubu 490, wanda ya zarta Afirka ta kudu, kasar da Bankin duniya yayi kiyasin tattalin arzikinta, ya kai dala miliyan dubu 384 a shekara ta 2012.
Kamar yadda zaku ji cikin wannan rahoto da Nasiru Adamu El-Hikya ya aiko mana.