Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Senegal sun saki mutane 4 da aka zarga da kulla makarkashiyar juyin mulki wa shugaba Abdoulaye Wade


Abdoulaye Wade (File photo)

Hukumomin Senegal sun saki mutane 4 da aka zarga da kulla makarkashiyar juyin mulki wa shugaba Abdoulaye Wade, su na masu fadin cewa babu wata kwakkwarar shaidar da zata sa a ci gaba da rike su. Kakakin gwamnati, Moustapha Guirassy, ya fada jiya talata cewa a bayan binciken farko da aka gudanar, ba a ga wata shaida tartibiya cewa mutanen su na shirya juyin mulki ba.

Hukumomin Senegal sun saki mutane 4 da aka zarga da kulla makarkashiyar juyin mulki wa shugaba Abdoulaye Wade, su na masu fadin cewa babu wata kwakkwarar shaidar da zata sa a ci gaba da rike su. Kakakin gwamnati, Moustapha Guirassy, ya fada jiya talata cewa a bayan binciken farko da aka gudanar, ba a ga wata shaida tartibiya cewa mutanen su na shirya juyin mulki ba. Guirassy yace an saki mutanen daren litinin, koda yake yace har yanzu ba a rufe wannan batun ba. A ranar asabar ne ministan shari’a na Senegal, Cheikh Tidiane Sy, ya fada ta gidan telebijin na kasar cewa mutanen sun so kai hare-hare kan wasu cibiyoyi, ciki har da wata kasuwa dake cika da mutane a tsakiyar birnin Dakar. Wannan sanarwa ta zo jim kadan kafin dubban mutane su yi zanga-zangar nuna kin jinin shugaba Wade da kuma munin yanayin rayuwa a birnin na Dakar. ‘Yan zanga-zanga da yawa sun ce zargin da gwamnatin ta yi cewa ana kulla makarkashiyar juyin mulki, wani yunkuri ne kawai na share kafar wannan zanga-zanga. An yi wannan zanga-zanga a ranar cikar shekaru 11 da hawan shugaba Wade kan mulki. An yti zanga-zangar a dandalin ‘yanci na Dakar, dandalin da masu zanga-zangar suka yi wa lakabi da sunan Tahrira, watau sunan dandalin nan na al-Qahira da ya zamo cibiyar masu tunzurin da suka kawar da shugaban Masar daga kan mulki.

XS
SM
MD
LG