Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana ci gaba da barin wuta a Tripoli babban birnin kasar Libya


Wata tankar mai tana cin wuta a bayan birnin Ajdabiya, dake kudancin Benghazi, Libya.

An goce da barin wutar bindigogin kabo jiragen sama, aka kuma yi ta jin fashe-fashe a dare na uku a jere a Tripoli babban birnin Libya a daren litinin.

An goce da barin wutar bindigogin kabo jiragen sama, aka kuma yi ta jin fashe-fashe a dare na uku a jere a Tripoli babban birnin Libya a daren litinin, yayin da Amurka da kawayenta suke kokarin fadada garkuwa a samaniyar kasar dake Afirka ta arewa. Gidan telebijin na Libya yace jiragen saman kasashen taron dangi sun kai sabbin hare-hare a kan birnin, amma kasashen na yammaci ba su ce uffan ba game da ko sun kaddamar da sabbin hare-hare a kan Tripoli. Wani kakakin gwamnatin Libya, Moussa Ibrahim, yace an kai hari kan filin jirgin saman birnin Sebha na kudancin kasar, da kuma wani yankin da ake kira Kilomita 27 a yamma da Tripoli. Wannan wuri yana kan hanyar motar da ta bi ta bakin gabar teku ta hade babban birnin da garin Zawiya wanda askarawan gwamnati suka kwace daga hannun ‘yan tawaye a farkon watan nan. Wannan wuri da ake kira Kilomita 27, sansani ne na wasu zaratan sojojin da ake kira Birged din Khamis dake karkashin jagorancin daya daga cikin ‘ya’yan shugaba Muammar Gaddafi. Jiya litinin din kuma, daruruwan magoya bayan Gaddafi sun yi cincirindo a hedkwatarsa dake Bab Azizya, domin hana kai harin bam a kan wurin, inda suka rika taka rawa su na karkada tutoci masu launin kore.

Janar Carter Ham na sojojin Amurka, wanda ke jagorancin wannan farmakin soja, yace kasashen taron dangi zasu fadada yankin da jirage ba zasu yi shawagi cikinsa ba daga samaniyar Benghazi na agabashin kasar zuwa Brega mai matatar mai a bakin teku, har zuwa Tripoli. Yace nan bada jimawa ba zasu fara yin sintiri da jiragen sama a duk tsawon yankin arewacin kasar Libya domin tilasta aiki da kudurin Majalisar Dinkin Duniya na makon jiya wanda ya bada iznin daukar matakan soja domin hana shugaba Gaddafi kai hari kan fararen hula masu adawa da shi. A can wani gefen kuma, mayakan ‘yan tawaye da suka yi kokarin sake kwato garin Ajdabiya na gabashin kasar sun sha kashi jiya litinin. ‘Yan tawayen suka ce sojojin Gaddafi wadanda har yanzu suke rike da hanyoyin shiga birnin sun fatattake su da rokoki da wutar tankokin yaki.

XS
SM
MD
LG