Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa Na Nijar Da Najeriya Sun Kulla Wata Yarjejeniya


NIGER NIGERIA HALCIA 2019
NIGER NIGERIA HALCIA 2019

Hukumar yaki da cin hanci ta jamhuriyar Nijer wato HALCIA da takwararta ta Najeriya wato EFCC sun rattaba hannu akan wata yarjejeniya a yau a birnin yamai da nufin farautar mahandama a kasashen biyu makwaftan juna.

Lura da yadda mahandama dukiyar jama’a ke amfani da hanyoyin kasa don boye abubuwan da suka wawure a kasashensu na asali ya sa hukumar HALCIA da takwarar ta Najeriya EFCC kulla yarjejeniya wace a karkashinta Najeriya da Nijer zasu yi aikin hadin guiwa da zummar tunkarar wannan kalubale inji shugaban hukumar EFFCC Ibrahim Magu.

Shugaban hukumar yaki da cin hanci ta HALCIA mai shara’a ABDOURAHMAN GHOUSMAN ya bayyana cewa yarjejeniyar hukumomin biyu za ta yi tasiri sosai a yakin da suka kaddamar da barayin dukiyar jama’a…

Shugaban hukumar yaki da cin hanci ta HALCIA mai shari’a Abdourahaman Ghousman ya bayyana cewa yarjejeniyar hukumomin biyu za ta yi tasiri sosai a yakin da suka kaddamar akan barayin dukiyar jama’a.

Kamar yadda gwamnatoci ke kara tsaurara matakan dakile hanyoyin cin hanci haka su ma mahandama dukiyar jama’a ke kokarin bullo da dabarun kaucewa dukkan wani tarkon da aka dana, sabili kenan da shugaban reshen transparency international a Nijer Mamman Wada ke gargadin mahukunta.

Rahoton Transparency International na shekarar da ta gabata ya saka Nijer da Najeriya a sahun kasashen da suka yi wani dan karamin hobbasa akan maganar yaki da cin hanci yayinda kungiyoyin cikin gida ke kallon dalilan siyasa a matsayin wani tarnakin da ke hanawa jami’an yaki da cin hanci motsawa.

Ga karin bayani cikin sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:11 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG