Accessibility links

An kashe wani Malami a jihar Borno

  • Jummai Maiduguri

Irin barnar da hare haren yan kungiyar Boko haram ke nan.

‘Yan sanda Nigeria sunce wasu wadanda ake zaton yan kungiyar Boko Haram ne sun harbe wani sannanen Malami a arewa maso gabashin kasar.

‘Yan sanda Nigeria sunce wasu wadanda ake zaton yan kungiyar Boko Haram ne sun harbe wani sananen Malami a arewa maso gabashin kasar.

Jiya asabar yan sanda suka ce a ranar juma’a aka harbe Mallam Liman Bana dan shekara sittin da biyar bayan salar Isha a garin Ngala jihar Borno. Jami’ai suka ce yan bindigan sunje ne akan babura kuma suka arce bayan da suka kai harin.

Jami'ai sun dora laifin wannan kisa akan yan kungiyar Boko Haram, wadda take kai hare hare, yawanci a arewa masu gabashin Nigeria. Ana kyautata zaton kungiyar ce keda alhakin kai hare hare akan yan sanda da yan siyasa da shugabanin jama’a da kuma Malamai.

XS
SM
MD
LG