Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ilimi Mabudin Rayuwa!


A kasar Amurika, akwai hanyoyin bawa yara ‘yan framari da sakandari ilimi ta hanyoyi masu dama. Wadannan hanyoyin sun hada da Makarantu, da Makarantar Gida wadda ake cema Homeschooling a turance.

Wato shidai irin wannan tsarin, yara sukan zauna a gida da iyayensu zasu shiga makaranta ta yanar gizo, kuma zasu gana da malamansu, kamar yadda ake ganawa da yara a makarantu.

Har su gama sheharunnan shida na framari da sakandire basu da bukatar suje aji. Wannan tsarin yana taimakawa matuka wajen tarbiyyar yara wanda suna gaban iyayensu a kowane lokaci.

Daga shekarar 1999 zuwa yau an samu Karin yawan yara masu makarantar gida da yakai kimanin kashi 75% wanda kuma yayi daidai da kashi 4% na yawan dalibai a kasar Amurika baki daya.

XS
SM
MD
LG