Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Imo: ‘Yan bindiga Sun Kai Hari Na Uku Cikin Mako Daya 


'Yan Bindiga Suka Yi Hedikwatar 'Yan Sanda A Owerri
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:12 0:00

'Yan Bindiga Suka Yi Hedikwatar 'Yan Sanda A Owerri

Wannan hari na zuwa ne kwana guda bayan nada sabon mukaddashin shugaban ‘yan sandan Najeriya Usman Alkali Baba, wanda ya maye gurbin Mohammed Adamu.

‘Yan bindiga​ sun sake far wa wani ofishin ‘yan sanda a jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya inda suka sake mutanen da ake tsare da su.

Maharan sun kuma yi garkuwa da wani dan sanda daya, kamar yadda rahotanni ke nunawa.

‘Yan bindigar sun kai harin ne a hedikwatar ofishin ‘yan sanda da ke Mbieri a karamar hukumar Mbaitoli da safiyar Alhamis a jihar ta Imo.

Rahotanni a Najeriyar sun ce ‘yan sandan da ke hedikwatar sun yi dauki ba dadi da maharan, amma sun fi su, saboda muggan makamai da ‘yan bindigar ke dauke da su a lokacin da suka kai harin.

Bayanai sun tuna cewa, baya ga sace dan sanda daya da aka yi a harin, an kuma jikkata wasu jami’an tsaron biyu.

'Yan Sandan Najeriya
'Yan Sandan Najeriya

Wannan shi ne karo na uku cikin mako guda, da ‘yan bindiga ke kai hari a ofisoshin ‘yan sanda a jihar.

Harin na zuwa ne kwana guda bayan wani da aka kai akan hedikwatar ‘yan sanda da ke karamar Ehime Mbano a Imon.

Karin bayani akan: ‘yan bindiga​, Owerri​, Mohammed Adamu, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

Ya kuma zo ne sa’o’i bayan ziyarar da mataimakin shugaban kasa Prof. Yemi Osinbajo tare da tsohon Sufeton ‘yan sanda Najeriya, Mohammed Adamu suka kai a Owerri​.

Kazalika a farkon makon nan, ‘yan bindiga sun kai hari a hedikwatar ‘yan sanda da gidan yarin birnin, inda suka kubutar da fursunoni sama da 1,800 kamar yadda rahotanni suka nuna.

Yadda maharan suka fasa gidan yarin Owerri
Yadda maharan suka fasa gidan yarin Owerri

Wannan hari har ila yau ya salwantar da kusan daukacin motocin jami'an tsaro da ke harabar ofishin ‘yan sandan.

Hukumomi a jihar ta Imo na zargin kungiyar IPOB mai fafutukar kafa kasar Biafra da kai wadannan hare-hare, zargin da kungiyar ta musanta.

Tsohon hoto: Wasu magoya bayan IPOB
Tsohon hoto: Wasu magoya bayan IPOB

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari wanda ya je London don ganin likita, ya yi Allah wadai da wadannan hare-hare, ya kuma ba jami’an tsaron kasar umurnin su yi iya bakin kokarin wajen ganin sun cafke maharan.

Wannan hari na baya-bayan nan na zuwa ne kwana guda bayan da aka nada sabon mukaddashin shugaban ‘yan sandan Najeriya Usman Alkali Baba, wanda ya maye gurbin Mohammed Adamu.

Yadda Aka Yi wa Sabon Mukaddashin Sufeton 'Yan sandan Najeriya Usman Alkali Baba Kwalliyar Karin Girma
Yadda Aka Yi wa Sabon Mukaddashin Sufeton 'Yan sandan Najeriya Usman Alkali Baba Kwalliyar Karin Girma

A ranar Laraba sabon mukaddashin Sufeton ‘yan sanda ya shiga ofis.

Masu sharhi na cewa daga cikin manyan kalubalan da zai fuskanta, akwai matsalar masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa da kuma ‘yan awaren kungiyar ta IPOB.

Baya ga wadannan matsaloli, Najeriya har ila yau na fama da rikicin Boko Haram a arewa maso gabashin kasar wanda aka kwashe sama da shekara 10 ana yi.

XS
SM
MD
LG