Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

"Ina Mai Allah Wadai Da Kisan 'Yan Arewa A Kudu" - Buhari


Shugaba Buhari (Facebook/Gwamnatin Najeriya).
Shugaba Buhari (Facebook/Gwamnatin Najeriya).

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da yadda ake samun rahotannin kai hare-hare kan ‘yan arewa dake zaune a kudancin kasar.

A baya-bayan nan ‘yan arewacin Najeriya dake kasuwanci a kudancin kasar sun shiga cikin fargaba sosai, bayan rahotannin kisan wasu ‘yan kasar Nijar takwas a Owerri babban birnin jihar Imo.

An zargi kungiyar dake fafutukar kafa kasar Biafra – IPOB da alhakin kashe mutanen, lokacin da ‘yan bindiga na kungiyar suka kai hari wani gida da Hausawa na Najeriya da Nijar ke zama a ciki.

A cikin wata sanarwa da kakakin shugaba Buhari, Malam Garba Shehu ya fitar, shugaban Najeriyar ya sha alwashin yin duk mai yiwuwa wajen gudanar da bincike cikin gaggawa domin gurfanar da wadanda suka aikata wannan aika-aika a gaban kotu.

Shugaba Buhari ya ce kisan gillar da aka yiwa mutanen ba abu ne da gwamnati za ta amince da shi ba, sannan ya bukaci al’umma da malaman addini da su kara daga murya don yin Allah wadai da kashe-kashen.

Ya bayyana yadda gwamnatinsa ke kokarin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin kudu maso gabas da ma kasa baki daya, inda ya ce rahotannin kashe-kashe a ko’ina abin bakin ciki ne da rashin jin dadi.

'Yan Binga a Najeriya
'Yan Binga a Najeriya

Shugaban ya kuma mika ta’aziyyarsa ga iyalan jami’an tsaro da aka kashe da kuma gwamnati da al’ummar Jamhuriyar Nijar da maharan suka yi wa ‘yan kasarsu kisan gilla.

A wani labari mai dadi kuma, rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta ce jami’anta sun samu nasarar kubutar da wasu mutane da aka yi garkuwa da su a jihar.

Rundunar ta ce ta kubutar da mutanen su kimanin shida ne a kauyen Tandama, yayin wani samame da jami’anta suka kai a maboyar ‘yan ta’adda a karamar humar Danja.

Cikin wata sanarwa, kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Gambo Isah ya ce bayan sirri da suka samu bayan sun kai wani samame a maboyar ‘yan ta’adda a kauyen Tandama ne ya taimaka wajen samun sanarar kubutar da mutanen.

XS
SM
MD
LG