Yadda Muka Yi Rayuwa A Hannun Masu Garkuwa-Fasinjar Jirgin Kasa

Daya daga cikin fasinjojin jirgin kasar Kadauna-Abuja da mahara su ka saki a baya bayan nan ya bayyana yadda su ka yi rayuwa a hannun 'yan bindigar,
Kaduna, Nageria —
Malam Muktar Shu'aibu daya daga cikin mutane biyar da 'yan-bindiga su ka saki ranar Talata, ya ce sun yi fama da rashin lafiya da kuma zaman zullumi na rashin sanin makomar su a daji lokacin da su ke hannun 'yan-bindigan.
A hirar shi da Muryar Amurka, Shu'aibu wanda aka samu yana zaune cikin 'yan'uwan shi da masu zuwa don jajantawa, ya ce masara su ke ci safiya da rana sai kuma a daidaikun ranaku akan kawo musu shinkafa. Ya ce faifan bidiyon da aka nuna 'yan-bindigan na dukan su gaskiya ne amma fushi su ka yi sakamakon hana 'yan'uwan wadanda aka sacen zuwa dajin don karbo su.
Game da harbin Al'amin Muhammad kuwa malam Muktar Shu'aibu ya ce kuskure aka yi kuma yanzu ya na cikin wadanda aka sako ranar Talata. Ya ce har yanzu akwai mutane 34 a daji ba a sako su ba. Ya ce sau biyu 'yan-bindigan na basu naira dubu goma-goma don su kashe . Ya kuma bayyana cewa, a gidan shugaban 'yan-bindigan da ke cikin dajin su ke sayen abun da su ke sha'awa.
Saurari cikakkarkar hirar shi da Isa Lawal Ikara cikin sauti:
Labarai masu alaka
‘Yan Bindiga Sun Saki Wani Bidiyo Da Suke Azabtar Da Mutanen Da Suka Sace
Duk Wani Mai Kishin Najeriya Dole Ya Nemi A Daidaita Tikitin Dan Takara Da Mataimakinsa - Kwankwaso
AU Ta Ba Da Gudummawar Kayan Aiki Na Yaki Da ‘Yan Boko Haram A Yankin Tafkin Chadi
Saudiya Ta Taso Koyar Wasu Maniyyatta ‘Yan Jihar Kano Masu Biza Ta Bogi
Za ku iya son wannan ma
-
Agusta 07, 2022
"Ina Mai Allah Wadai Da Kisan 'Yan Arewa A Kudu" - Buhari