Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Garkuwa Daliban Islamiyyar Tegina Na Neman Naira Miliyan 150 Kudin Fansa


Yan bindigar da suka yi garkuwa da daliban Islamiyyar Salihu Tanko 148 a garin Tegina ta Karamar Hukumar Rafin jihar Nejan Nigeria sun ce sai an biya Naira miliyan 150 a matsayin kudin fansa kafin su sako yaran da akasarinsu yan kasa da shekaru 13 ne.

A yanzu dai kimanin kwanaki 10 kenan da wadan nan 'yan bindiga suk ayi dirar mikiya a garin na Tegina tare da kwashe wadan nan dalibai bayan da suka hallaka mutun guda da rana tsaka.

A wani taron Manema Labarai a makon jiya, Mataimakin Gwamnan jihar Nejan Alh. Ahmed Muhammad Ketso, ya ce duk da ya ke gwamnatin jihar na kokarin kubutar da yaran amma gwamnati ba ta da niyyar biyan kudin fansa ga yanbindigar.

Karin bayani akan: Tegina, dalibai, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

A yanzu dai masu sharhi akan al’amurra na ci gaba da jefa ayar tambaya akan yadda kungiyoyi musamman na kasa da kasa su ke nuna rashin damuwa sosai akan daliban Islamiyah dake daji a hannun ‘yanvbindigar.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:50 0:00

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG