Wata yarinya mai shekaru 17 da haifuwa da aka cinna mata wuta bayan an yi mata fyade a gabashin India tana kwance a asibiti rai hannun Allah, yayin da rabin jikinta ya kone a fadar jami’an kiwon lafiya.
An kaiwa wannan matashiya hari ne a ranar Juma’a, bayan fyade da aka yiwa wata yar shekaru 16 kana aka konata har lahira a cikin jiha guda wato Jharkhand.
'Yan sanda sun kama wani mutum mai shekaru 19 da suke kauye daya da yarinyar mai shekaru 17. An ce shi ne ya zuba mata kanazir kana ya cinna mata wuta yayin da taki yarda ya yi lalata da ita.
Ana zargin wasu, mutane hudu da yin garkuwa da kuma fyade da wata yarinyar mai shekaru 16 a makon da ya gabata. Bayan an wayi gari iyayen yarinyar sun kai kara ga dattijan kauyen inda aka ci mutanen tarar kudi. Jami’ai sun ce mutanen hudu sun fusata da wannan tarar dala dari bakwai da hamsin da aka dora musu, a kan haka suka cinna wuta a gidan su yarinyar yayin da take ciki domin suka kasheta.
Facebook Forum