Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen Indiya Da Pakistan Zasu Yi Atisayin Soja Na Hadin Gwuiwa


Wasu sojojin Indiya

India da Pakistan kasashe biyu a yankin Asiya da suka mallaki makaman nukiliya da kuma suke gaba da juna har ma sun sha gwabza yaki, zasu yi atisayin soji na hadin gwuiwa

Yanzu haka dai a wani mataki na ba saban ba ko kuma matakin da ba’a taba gani ba, Kasashen yankin kudancin Asiya biyu masu karfin makaman nukiliya kasar India da Pakistan zasu fara wani atisayen soja na hadin gwiwa.

A cikinmakon data gabata ne ministan tsaron India,Nirmala Sitharaman ya tabbatar da cewa India zata bi sahun atisayen yaki da da ‘yan taadda ita da kasar Pakistan.

Sai dai wannan shine karo na farko da za aga kasahen biyu da aka rabu tun a shekarar 1947, sun yarda da juna kuma harma zasu yi wani abu wuri guda karkashin kungiyar kasashen dake yankin kudancin Asiya a Karkashin kulawar Rasha kumaa cikin watan Agustta ne za ayi wannan atisayen

Ita dai wannan kungiyar ta tattalin arziki da tsaro da bunkaa demokaradiyya an samar da it ace a Shanghai na kasar China a shekar 2011, kuma kasashen da sukecikn ta sun hada da China,India,Kazakhastan,Pakistan,Russia,Tajikistan sai kuma Uzbekistan

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG