Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

INDONESIA: Babu Wanda Ya Rayu daga Jirgin da Ya Fado


Masu aikin ceto rai a wurin da jirgin ya fadi

Jami’an Indonesiya yau Talata sun ce babu wanda ya rayu daga hadarin jirgin sama na Lahadin nan da ta gabata a gabashin kasar.

Sai yau Talata ma’aikatan agaji da ceto suka isa inda jirgin ya fadi a lardin Papua, bayan fuskantar kalubale daga rashin kyawun hanya. Sun kuma bayyana cewa jirgin ya far-farshe baki dayansa.

Jami’ai sun bayyana cewa masu ayyukan agaji sun samo gawarwakin mutane 53 a cikin 54 dake cikin wannan jirgi na Tri-gana Air mai lambar tafiya 267. Ya fadi jim kadan kafin lokacin da ake sauraron saukarsa a garin Oksibil.

Banda fasenjoji da ma’aikata da ke cikin sa, jirgin na kuma dauke da kudaden gwamnati dala dubu 470 da ake shirin rabawa iyalai marasa karfi.

Shugaba Joko Widodo ya gayawa manema labarai bayan fashewar cewa ya baiwa Ma’aikatar Sufuri umarnin bunkasa tsaro a harkokin jiragen sama domin kiyaye hadura nan gaba.

Ma’aikatar harkokin jiragen sama ta Indonesiya ta shiga tsaka mai wuya a kwanakin bayannan, saboda yawaitar hadura a ciki harda faduwar jirgin AirAsia wanda ya kashe mutane 162. Wannan kasa dake yankin Pacific na daya daga cikin kasashe a nahiyar Asiya dake bunkasa ta fannin sufurin jiragen sama, amma ta na fama da karancin kwararrun matuka, da masu gyara, har da jami’ian kula da zirga-zirgar jiragen sama domin tabbatar da tsaro.

Kamfanin Trigana ya fuskanci munanan hadura 14 tun bayan kafuwarsa a shkeara ta 1991, kuma yana daya daga cikin jiragen saman Indonesiya da aka haramta wa shiga sararin samaniyar Tarayyar Turai.

XS
SM
MD
LG