Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Kula da aukuwar bala'o'i a Indonesia sunce girgizar kasa da ta haddasa mummunar igiyar ruwa sun kashe kusan mutane dari uku.


Wani mutum a kasar Indonesia yake goye da dansa cikin ambaliyar ruwa da girgizar kasa da mummunar igiyar ruwa da kasar take fama da shi.

Bugu da kari wani tsauni da yake ta ribibi cikin 'yan kwanakin nan da ya fara aman wuta ya kona mutane talatin a tsibirin Java.

Jami’an dake kula bala'o'i a kasar Indonesia, sunce girgiza kasa da mummunar igiyar ruwa a Sumatra sun kashe kusan mutane dari uku, kuma kusan mutane talatin sun mutu a sakamakon amon wuta a tsibirin Java.

A karon farko a yau Laraba ma’aikatan agaji da jiragen sama da kuma jiragen sama masu saukar ungulu suka isa tsibirran na Mentawai da suke lungu a gabar tekun Sumatra daga yammaci inda a ranar litinin mumunar igiyar ruwa da ta biyo bayan girgizar kasar, sun yi awon gaba da wasu kauyuka.

Shugaban kasar, Susilo Bambang Yudhoyono, ya katse ziyarar daya kai Vietnam ya koma gida domin nazarin aiyukan ceto.

Jimmy Nadapdap,shine ke lura da yunkurin aiyukan ceto na kungiyar agajin kasa da kasa, World Vision. Jimmy yace a shirye suke da kayayyakin taimako.

Yace suna da kayayyakin da suka adana a birnin Jakarta da kuma birnin Padang, domin su samu damar aikawa da kayayyakin abinci da ruwa da kuma kayayyakin taimakon yara cikin gaggawa.

XS
SM
MD
LG