Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

INEC Ta Mika Bukatar Yin Zabe Ta Na'ura Gaban Majalisa


Shugaban Hukumar zaben Najeriya Mahmoud Yakubu

Shugaban hukumar zabe ta Najeriya, INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya mika bukatar a sauya yanayin gudanar da zabe daga tsarin jefa kuri’a a zahirance da ake amfani da shi yanzu zuwa na na’ura wato electronic voting a gaban majalisar wakilai.

A tsawon shekarun da suka gabata, akasarin ‘yan Najeriya suna son a yi amfani da tsarin zabe mai inganci saboda kura-kuran da suka kawo cikas ga zabukan da suka gabata wadanda suka hada da, satar kuri’u, tursasawa masu jefa kuri’a, satar akwatunan zabe, badawa da karbar cin hanci a yayin zabe, tashin hankali da tafka magudi a sakamakon zabe, lamarin da ya jawo suka ga hukumar INEC a lokutan zaben baya.

Da yake bayyana dalilin mika bukatar komawa tsarin zaben na’urar zamani da farfesa Mahmud ya yi a gaban kwamitin majalisar wakilan kasar, daraktar yada labaran INEC, Mallam Nick Dazang ya bayyana cewa yana ganin idan aka koma amfani da na’ura zai inganta zabu kanmu, kuma zai rage magudi da ake tafkawa locacin zabe.Ya kuma bayyana cewa sabon tsarin zai magance matsalar samun wadansu su kada musu kuri’a.

Idan ba’a manta ba a shekarar 2007 ne Hukumar INEC ta gabatar da fasahar daukar bayanan masu jefa kuri’a kai tsaye wato Direct Data Capture Machine technology da ya kai ga samar da rijistar masu kada kuri’a ta na’urar zamani da fasahar karanta katin zabe wato card reader wanda aka yi ta amfani da su a lokutan zabe tun lokacin ya zuwa yanzu lamarin da wasu ‘yan Najeriya su ka ce ya inganta yanayin zabe.

Masana sha’anin zabe dai na hasashen cewa idan aka aiwatar da tsarin zabe ta na’urar zamani ko yanar gizo yadda ya kamata zai taimakawa kasar wajen gudanar da ingantaccen zabe tare da kawo karshen muggan dabi’u da ake tafkawa a lokutan zabe.

Saurari cikakken rahoton Halima Abdulra’uf a cikin sauti:

INEC ZATA FARA ZABE A NA'URA
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:01 0:00


Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG