Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

INEC Ta Tabbatarwa Da Majalisar Kasa A Shirye Take Da Babban Zabe Mai Zuwa


INEC
INEC

Majalisar shugabannin Najeriya mai ikon fada a ji tace za a gudanar da zabe ranar 14 ga watan Fabrairu kamar yadda aka tsara.

Majalisar ministoci da shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ke jagoranta, da ta kunshi janar -janar, da ‘yan majalisar dokoki da kuma tsofaffin shugabanni, ta sanar da shawarar da ta tsaida bayan zamanta a babban birnin tarayya Abuja jiya Alhamis.

Wadansu ‘yan Najeriya sun nemi a janye ranar zaben sabili da tafiyar hawainiya da aikin raba katin zabe na din din din yake yi, da kuma tashin hankali da ake fama da shi a arewa maso gabashin kasar inda dakaru suke arangama da mayakan Boko Haram.

Gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha, yace mahalarta taron sun tattauna kan wadannan batutuwan, amma sun kuma ji ta bakin hukumar zabe mai zaman kanta.

Kamar yadda kuka gani, daya daga cikin zaman majalisar zartarwa na ba sabanba, da ya dauki sama da sa’oi bakwai ana tattauna akan batutuwa masu sarkakiya, kan ko hukumar zabe ta kamala shirin gudanar da zaben ko babu, ko kuma akwai bukatar daga ranar zaben.

Rahotanni dake fitowa daga hukumar zabe na nuni da cewa hukumar zaben a shirye take tsaf ta gudanar da zaben. Rudunar tsaro kuma ta bayyana damuwa kan wadansu kananan hukumomi ko zasu fuskanci kalubalar tsaro.

Amma hukumar zabe tana da ikon gudanar da zabe da ya hada da tsaida ranar zabe, saboda haka majalisar zartaswar ta tsaida shawara cewa, hukumar zabe ta bayyanawa kasa idan tayi shirin gudanar da zabe ta kuma cigaba, ta gudanar da zabe.

Kafin zaman dai, masu zanga zanga da jam’iyar hammayya ta APC sun yi kira da a gudanar da zaben kamar yadda aka tsara.

Shugaba Jonathan da jam’iyar PDP na fuskantar babbar kalubale daga jam’iyar APC da dan takararta, tsohon shugaban mulkin soja Muhammadu Buhari.

XS
SM
MD
LG