Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ra’ayoyin ofisoshin Kamfen din Jam’iyyu Kan Matakin Majalisar Kasa


Najeriya Zaben 2015 Buhari Jonathan
Najeriya Zaben 2015 Buhari Jonathan

An dai kawo karshen tababa da ake tayi akan maganar ‘dage babban zabe a Najeriya, kasancewar majalisar kasa ta cimma matsaya bayan da ta kwashe sa’o’i kusan tara tana gudanar da taro akan batun dage zaben.

Wannan kuduri dai ya biyo bayan tabbacine da shuganban hukumar zabe Farfesa Attahiru Jega, ya baiwa majalisar inda yace hukumar a shirye take da ta gudanar da zabe.

Wakiliyar mu Madina Dauda, ta tambayi mataimakin shugaban hulda da manema labarai Isa Tafida Mafindi yariman Muri, cewar yaya ofishin kamfe din shugaba Goodluck Jonathan, yaga wannan mataki da majalisar kasa ta dauka? Inda ya amsa mata da cewa, “mufa jam’iyya ce da kuma shugaban kasar mu da mataimakinsa masu hakuri, zamu baiwa Najeriyar mamaki, mu bamu da shakka akan zaben kuma kowanne lokaci akayi shi zamu ci ne.”

Sai kuma ofishin janal Muhammadu Buhari, inda mataimakiyar shugaban hulda da manema labarai Naja’atu Mohammed tace, “basu sukayi ba Ubangijine yake ikon sa, saboda kusan duk wadanda yanzu sukace dole ayi zabe, a da basu bi ra’ayin al’ummar su ba, nake yiwa Allah godiya domin wannan yakin nasa ne, kuma munyi Imani da shi” ta cigaba da cewa a yau Goodluck da jam’iyyar sune suke gudun ayi zabe.

Tsofaffin shuwagabannin kasa da gwamnonin jihohi ne suka halarci taron majalisar kasar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:44 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG