Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iran Ta Gargadi Amurka Kan Ficewa Daga Yarjejeniyar Nukiliya


Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani

Iran tayi wa Amurka gargadi kan ficewa daga yarjejeniyar nukiliya ta shekarar 2015

Sakataren harkokin wajen Birtaniya na kokarin yin kamun kafa wajen gwamnatin Shugaban Amurka, Donald Trump domin Amurka ta ci gaba da kasancewa a cikin yarjejeniyar shekarar 2015 da aka kulla tsakanin Iran da manyan kasashen duniya kan tsagaita harkokin nukiliyar ta domin saukaka ko cire takunkumin da aka saka mata.

Dangane da hakan ne, Boris Johnson zai tattauna da mataimakin shugaban kasar Amurka Mike Pence da mai bada shawara kan harkokin tsaron Amurka John Bolton a yau Litinin kuma maganar Iran na cikin manyan batutuwan da za’a tattauna akai, a cewar ofishin Johnson.

Shugaban Amurka na yawan sukar lamirin abinda ya kira yarjejeniya maras kyau wacce a ranar 12 ga watan Mayu zai yanke hukunci kan ko zai sabunta ta ko kuma ficewa daga cikinta..

A jiya lahadi ne Shugabn kasar Iran Hassan Rouhani ya bayyana cewa idan Amurka ta janye daga yarjejeniyar zata nadamar da bata taba yi ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG