Jiya Laraba aka kammala taron na shida na tsawon kwanaki biyu kan nuna goyon baya ga Intifada na Falasdinawa a Teheran, babban birnin Iran, a inda shugaban kasar yayi alkawarin bayar da karin taimako ga Falasdinawa dake yakar mamayar Isra’ila. Iran ta jima tana bayar da goyon baya na kudi da soja ga ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa.
Kafofin yada labarai na Iran sun ambaci shugaba Hassan Rouhani yana fadin cewa al’ummar Iran sun sadaukar da kai da dukiya sosai a baya don goyon bayan Falasdinawa da yin adawa da Isra’ila, amma kuma zasu ci gaba da wannan kudurin na tallafa musu. Kafofin labarai na Iran suka ce shugaba Rouhani yayi wannan furuci ne a lokacin da yake ganawa a gefen taron da shugaban majalisar kasa ta Falasdinu, Salim al-Zanoun.
Facebook Forum