Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ireland Ta Haramta Shigowa Kasarta Da Kayayyaki Daga Yankin Da Israila Ta Mamaye


Majalisar Dattawan Ireland da ta gabatar da kudurinhana shigowa da kayayyaki daga yankin yammacin kogin Jordan da Israila ta mamaye
Majalisar Dattawan Ireland da ta gabatar da kudurinhana shigowa da kayayyaki daga yankin yammacin kogin Jordan da Israila ta mamaye

Majalisar dattawan Ireland ta ayyana wata doka da ta haramta shigowa da kayayyakin da Israila ta sarafa daga yankin yammacin kogin Jordan da ta mamaye

A Ireland, majalisar dattijan kasar ta zartar da wata dokar da ta haramta shigo da kayayyaki daga sassan da Isra'ila ta mamaye a gabar yammacin kogin Jordan.

Idan majalisar wakilan kasar ta biyu sawun ta dattijai, Ireland zata zama kasar farko a turai da zata haramata kayayyaki da aka sarrafa a daga sassan da aka yiwa mamaya.

Sai dai dokar bata da goyon bayan gwamnatin kasar. Ministan harkokin wajen kasar Simon Coveney, yace aiwatar da dokar zata yi wahala, domin manufofin cinikayyar kasar yana tare ne da na kungiyar tarayyar turai watau EU. Ina mutunta wannan majalisa da shawarwarinta, amma da girmamawa ban goyi bayan wannan mataki ba," ministan ya gayawa majalisar dattijai.

Kuri'ar ta sami kakkausar suka daga hukumomin Isra'ila birnin Tel-Aviv.Ma'aikatar harkokin wajen Isra'ila ta soki majalisar dattijan Ireland saboda goyon bayan kuduri mai cike da hadari na msu tsatstsauran ra'yin masu yakin neman a kauracewa Isra'ila."

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Isra'ila Emmanuel Nahshon, yayi gargadin cewa, dokar zata yi nakasu ga matakan difilomasiyya na neman wanzar a zaman lafiya a gabas ta tsakiya."

Wani jigo a yankin Falasdinawa Aeb Erekat, yayi marhabin lale da labarin daga Ireland, ya kira shirin, a zaman "mataki na nuna baijita."

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG