Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ISIS Na Yiwa Falesdinawa Kisan Gilla aYarmouk cikin Syria


Wasu Falesdinawa a Yarmouk suna jiran tallafi

Ganin yadda kungiyar ISIS ke yiwa Falesdinawa kisan kiyashi a Yarmouk babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Mr. Ban Ki-moon yace dole a dauki matakan dakile aika aikar kungiyar.

Babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya Ban ki-moon yace ana bukatar daukar matakin gaggawa domin maganin yadda kungiyar ISIS ke yiwa ‘yan gudun hijiran Falasdinawa kisan kiyashi a sansanin Yarmouk, dake babban birnin kasar Syria da yanzu ISIS suka mamaye.

Mr. Ban ya yi kira da a tallafawa Falasdinawa ‘yan gudun hijira da aka rutsa a sansanin dake kudancin birnin Kudus.

Mr Ban yace, “lokaci ya yi da za a dauki kwararan matakan ceton rayuka da kuma mutunta bil’adama. Yace, ba zamu tsaya muna gani ana kisan kiyashi ba. Ba za a yi watsi da mutanen Yarmouk ba”.

Kimanin Palasdinawa dubu goma sha takwas ne suke zaune a sansanin lokacin da kungiyar IS ta kai hari makon jiya.

Sansanin da aka tsugunar da kimanin Palasdinawa‘yan gudun hijira dubu dari da saba’in yana karkashin gwamnatin Syria na kusan shekaru biyu, kuma agaji kalilan ne kadai suka samu.

A halin da ake ciki kuma, jiya Alhamis, wani babban jami’in Palasdinawa yace an cimma yarjejeniya da gwamnatin Syria na gudanar da ayyukan soji na hadin guiwa da nufin kakkabe mayakan ISIS daga sansanin.

Ahmed Majdalani yace, wata kungiyar bangaren Palasdinawa ta amince a ci gaba da tuntubar juna da shugabannin Syria, a kuma kafa dakarun hadin guiwa da gwamnatin.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG