Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iskar Teku Mai Karfi Ta Hallaka Mutane Da Lalata Dubban Gidaje A Bangladesh


Iskar teku mai karfin gaske dauke da ruwan sama, ta hauro kan doron kasa yau talata a yankin kudu maso gabashin Bangladesh, ta hallaka mutane biyu, ta lalata dubban gidaje.

Hukumomin kasar suka ce bishiyoyi da suka fadi sakamakon iska mai karfi da ruwan sama kamar da bakin kwarya su suka haddasa hasarar rayukan da aka samu.

Ana nuna fargaba kan 'yan gudun hijira na Rohingya su dubu 200 daga makwabciyar kasar Myanmar, wadanda suke wasu sansanoni inda muhallan basu da karfi sosai.

Gabannin afkawar iskar, hukumomin sun kwashe mutane kimanin dubu dari uku zuwa wasu wurare.

Hukumar kula da yanayi ta kasar tace iskar tana kadawar kilomita 117 cikin sa'a daya lokacin da ta hauro daga teku, amma ana sa ran karfinta zai ragu lokacinda take ci gaba da kadawa cikin kasar musamman ta arewaci.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG