Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Biyu Sun Rasa Rayukansu Sanadiyyar Kare Wasu Yara Musulmi


kwanaki bayan da Shugaba Donald Trump, ya gaya ma Shugabannin Musulmi cewa akwai muhimmncin hada kai don kawar da ta'addanci da tsattsauran ra'ayi.

Wani mutum cikin jirgi a birnin Portland na jihar Oregon, ta arewa maso yammacin Amurka, ya tsokani wasu matasa biyu Musulmi, sannan ya kashe wasu mutane biyu wadanda su ka nemi hana shi.

Martanin da ya biyo bayan wannan harin na ranar Jumma'a a yankin da kuma sauran sassan kasar, ya hada har da wani lafazi mai karfin gaske mai cewa irin wannan tsana ba ta da muhalli a cikin al'ummomin Amurka ko ma kasar baki daya.

'Yansandan Portland sun ce daya daga cikin 'yan matan da ke cikin jirgin na saye da hijabi, kuma wanda ya tsokane su din ya yi ta amfani da kalamai na nuna matukar tsana.

"Mutane biyu sun rasa rayukansu sanadiyyar kare wasu yara Musulmi daga kalamai na tsabar tsana a cikin wani jirgi da yamma," a cewar Magajin Garin Portland Ted Wheeler.

Gwamnar Oregon Kate Brown ta ce "wannan harin ya kada ni matuka."

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG