Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila Da Haddadiyar Daular Larabawa Za Su Maida Huldar Diflomasiyya


Firaminista Benjamin Netanyahu, yau Litini, ya ce kasar Isira’ila na shirin fara zirga zirgar jirgin sama kai tsaye da Hadaddiyar Daular Larabawa, ta wajen gitta sararin saman Saudiyya zuwa kasar, a matsayin wani bangare na dangantakar da aka kulla tsakanin Isira’ilar da Hadaddiyar Daular Larabawan.

Isira’ila da Hadaddiyar Daular larabawa sun sanar ranar Alhamis cewa, za su maido da huldar diflomasiyya karkashin wani tsari da Amurka ta jagoranta, wadda aiwatar da ita ka iya sake fasalin siyasar gabas ta tsakiya, kama daga batun Falasdinu zuwa rigimar da ake yi da Iran. Hadaddiyar Daular Larabawa za ta kasance kenan kasar Labarawa ta uku wajen shiga hulda da Isira’ila.

Netanyahu, wanda ya yi jawabi a Filin Jirgin Saman Ben-Gurion da ke birnin Tel Aviv, game da shirin fadada zirga zirgar jiragen saman, wadda annobar cutar corona ta shafa, bai yi bayanin lokacin da za a fara zirga zirga tsakanin Isira’ila da wannan kasar ta Larabawa ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG