Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila Ta Fitar Da Wadansu Dogarawa Daga Syria


masu aikin ceto rayuka a syria

Isra’ila ta kwashe kimanin dogarawan Syria masu aikin jinkai da ake kira White Helmet, da iyalansu, daga Syria, zuwa birnin Jordan jiya asabar da dare a cikin motocin safa karkashin rakiyar ‘yan sandan Isra’ila da motocin Majalisar Dinkin Duniya.

Ma’aikatar tsaron Isra’ila ta bayyana masu aikin ceton a matsayin farin kaya.Ta wallafa a shafinta na twitter cewa, “ an kwashe farin kayan daga inda ake yaki a kudancin Syria sabili da barazanar dake akwai ga rayukansu. Fitar da ‘yan kasar Syrian da suka rasa matsugunansu, da aka bi ta cikin Isra’ila wani aikin jinkai ne na ba sabanba.”

Ma’aikatar tsaron Isra’ila tace an kwashe mutanen ne bisa “bukatar da Amurka da wadansu kasashen turai suka gabatar”.

Isra’ila tace an kai mutanen zuwa wata kasa dake makwabta, amma bata ambaci Jordan ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG