Jiya Laraba tarzoma ta lafa akan iyakar Isira’ila da Gaza, a yayinda jami’an Palasdinawa suka ce Masar ta shiga tsakanin an kulla yarjejeniyar tsagaita bude wuta da Isira’ila.
Jami’an Isira’ila basu tabbatar da kula yarjejeniyar ba, amma sun ce idan ‘yan yakin sa kai a Gaza suka daina harbawa Isira’ila rokoki, itama Isira’ila zata kawo karshen hare haren da take kaiwa yankunan Palasdinawa.
Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman akan shirin samun zaman lafiya a gabas ta tsakiya, yayi gargadin cewa wannan itace tarzoma mafi muni da aka ganin tsakanin bangarorin biyu, tun rikicin shekara ta dubu biyu da goma sha hudu da aka yi tsakanin kungiyar Hamas da Isira’ila.
A yan watanin da suka shige, wakilin na Majalisar Dinkin Duniya ya sha yin kashedin cewa bangarorin biyu suna dab da fadawa cikin rikici
Facebook Forum