Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Israila Sun Kai Hare-hare Zirin Gaza Jiya Talata


Tankin yaki na Israila dake sintiri tsakanin iyakar kasar da Zirin Gaza
Tankin yaki na Israila dake sintiri tsakanin iyakar kasar da Zirin Gaza

Sojojin Isira'ila sun kai hare-hare jiya Talata a Zirin Gaza, inda su ka auna kungiyar mayaka ta 'yan rajin jahadi.

Hare-haren sun zo ne 'yan sa'o'i bayan da sojojin Isira'ila su ka ce mayakan sa kai a Gaza sun harba rokoki akalla 25 kan wasu wurare na kudancin Isira'ila.

Sojojin na Isira'ila sun ce makamin kariya ya cabcabke akasarin rokokin da aka harbo, to amma sojoji uku sun ji raunuka, wanda hakan ke janyo fargabar yuwuwar Isira'ila ta sake kai hare-haren ramuwa. Wata rokar ma ta fada kusa da wata makarantar kananan yara dab da lokacin da ta fashe.

Amurka ta kira taron gaggawa na Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, MDD, don tattauna hare-hare na baya-bayan nan daga Zirin Gaza. Ana kyautata zaton Kwamitin Sulhun zai yi taro a yau dinnan Laraba.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG