Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila Da Falasdinawa Sun Yarda Zasu Kara Tattaunawa


Shugabannin Isra'ila da Falasdinawa sun yarda za su fito da daftarin yarjejeniyar zaman lafiya, zasu kuma ci gaba da tattaunawa

Shugabannin Isra'ila da na Falasdinawa dake ganawa a Washington, sun yarda zasu zana wani daftarin yarjejeniyar zaman lafiya kammalalliya, zasu kuma sake ganawa nan gaba cikin wannan wata.

Wakilin Amurka a Gabas ta Tsakiya, George Mitchell, ya fada alhamis cewa daftarin zai zayyana irin sassaucin da ake bukata daga kowane bangare domin cimma kammalalliyar yarjejeniyar zaman lafiyar da zata warware dukkan muhimman batutuwa tare da kawo karshen rikici a tsakanin Isra'ila da Falasdinawa.

Wakilin na Amurka ya ce firayim ministan bani Isra'ila, Benjamin Netanyahu, da shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas, sun yarda za su sake ganawa a ranarkun 14 da 15 ga watan nan na Satumba a can yankin Gabas ta Tsakiya. Kamfanonin dillancin labarai sun ba da rahoton cewa watakila za a yi ganawar ta gaba a Masar wadda ita da kasar Jordan suek goyon bayan wannan yunkurin wanzar da zaman lafiyar.

Mitchell yace shi da sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton, zasu halarci tattaunawar ta gaba, wadda a bayanta, mashawartan Isra'ila da na Falasdinawa za su rika ganawa bayan kowane mako biyu.

Jami'an Amurka sun ce Mr. Netanyahu da Malam Abbas sun yi tattaunawa mai amfani alhamis din nan, tattaunawarsu ta farko a kusan shekaru 2. An kuma ce shugabannin biyu sun gana su biyunsu na tsawon mintoci 90.

XS
SM
MD
LG