Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Barack Obama Na Amurka Yace Bai damu Da Masu Cewa Shi Musulmi Ba Ne


A cikin wata hira da gidan telebijin na NBC, shugaban na Amurka ya yi magana kan tattalin arziki da kuma jita-jitar da wasu ke yadawa kan addininsa da inda aka haife shi.

Shugaba Barack Obama na Amurka yace tattalin arzikin Amurka yana bunkasa amma kuma bai kai mizanin da ake bukata ba.

A cikin wata hirar da yayi da gidan telebijin na NBC a jiya lahadi, Mr. Obama yayi kira ga majalisar dokokin Amurka da ta zartas da wasu daga cikin kudurorin da ya riga ya gabatar mata kamar na gaggauta samar da rance ga kananan kamfanoni tare da rage nauyin haraji ma kamfanoni.

Yace duk wata dokar da zata taimakawa kananan kamfanoni wajen samun rance zata ba su kwarin guiwar kara zuba jari. Shugaban na Amurka yace babu wani siddabarun da ake da shi na warware matsalolin tattalin arzikin kasar nan baki daya.

Har ila yau, Mr. Obama ya fadawa gidan telebijin na NBC cewa bai damu da kuri’ar neman ra’ayoyin jama’a da aka buga kwanakin baya wadda ta nuna cewa kimanin kashi 20 cikin 100 na Amurkawa sun yi imani da cewa shi Musulmi ne ba, duk da cewa shi Kirista ne kuma yana zuwa Coci, sannan ya sha nanatawa a bainar jama’a cewa shi Kirista ne.

Har ila yau, yace bai damu da rade-radin da ake bazawa kan cewa shi ba haifaffen Amurka ba ne, yana mai cewa “ba zan manna takardar shaidar haihuwa ta a goshi na ina yawo da ita ko yaushe ba.”

XS
SM
MD
LG