Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mataimakin Shugaban Amurka Joe Biden Yana Iraqi


A yau talata Amurka zata kawo karshen dukkan ayyukan farmaki a kasar Iraqi, daya daga cikin alkawuran da shugaba Barack Obama yayi a lokacin yakin neman zabe

Mataimakin shugaban Amurka Joe Biden ya sauka a birnin Bagadaza litinin da maraice, a yayin da Amurka ta ke shirin kawo karshen dukkan ayyukan farmaki a kasar ta Iraqi daga yau talata.

Wani jami'in ofishin jakadancin Amurka ya fadawa 'yan jarida cewa Biden ya sauka a babban birnin na Iraqi da misalin karfe 6 na yammaci agogon kasar. An shirya zai tattauna da shugabannin Iraqi a yau talata, kan yadda matsayin Amurka a kasar zai kara gusawa ga na diflomasiyya kawai.

Shugaba Barack Obama zai yi jawabi ga Amurkawa yau talata daga fadarsa ta White House kan wannan batu na janye sojojin Amurka daga Iraqi.

Daga cikin sojojin Amurka dubu 170 dake Iraqi a tsakiyar tura karin sojojin da aka yi a shekarar 2007, yanzu wadanda suka rage baki daya bai kai dubu hamsin ba. A bayan hakan kuma, sojojin Amurka ba zasu kai farmaki a kasar ta Iraqi ba sai idan sojojin Iraqi sun bukace su kuma za su tafi tare da su.

An cimma wannan sabon gaccin ne a yayin da ake ci gaba da samun daurin gwarman siyasa a Iraqi a kan kafa sabuwar gwamnatin da zata jagoranci kasar nan gaba.

XS
SM
MD
LG