Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila Ta Tallafawa Jama'ar Jihar Arewa Mai Nisa, Kasar Kamaru


Kasancewar halin kakanikayi da jihar arewa mai nisa ta kasar Kamaru ke ciki sanadiyyar hare haren da ‘yan kungiyar Boko haram da suka addabi jihar, jikadan kasar Isra’ila dake birnin Yawunde yace kasar sa zata tallafawa jama'ar jihar.

Jikadan ya bayyana hakan ne a wata ziyara da ya kaiwa majalisar wakilan kasar ta Kamaru ya bayyana masa irin agajin da kasar ta Isra’ila zata kai wa jihar Arewa mai nisan.

Jakadan ya bayyana cewa sun yi niyyar taimakawa jihar arewa mai nisa da ruwan sha mai tsabta da sha’anin noma da kiwo da kuma sha’anin kamun kifi, kuma ya kara da cewa zasu taimaka wajan bunkasa harkokin ilimi da karfafa harkokin tattalin arzikin jihar.

Jikadan ya kara da cewa irin ta’adin da ‘yan kungiyar boko haram suka yiwa jihar, ya zama wajibi a taimakawa mahukuntar domin ganin sun kammala da ‘yan kungiyar ta boko haram a fadin kasar baki daya.

Daga karshe ya bayyana cewa kasar Kamaru na bukatar taimako daga kasashe kawayen ta musamman a wannan lokaci da al’ummar kasar ke cikin tsaka mai wuya.

XS
SM
MD
LG