Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ISWAP Ta Kashe Baturen 'Yan Sanda A Borno


Da yake tabbatar da mutuwar DPOn a yau Laraba, kakakin rundunar 'yan sanda jihar Borno, Nahun Kenneth, yace har yanzu rundunar na tattara bayanai akan harin.

Mayakan kungiyar ISWAP sun hallaka baturen 'yan sanda (DPO) mai kula da shiyar Sabuwar Marte a Karamar Hukumar Marte ta jihar Borno.

Rahotanni sun bayyana cewar an hallaka DPOn mai mukamin sufurtanda ne a daren ranar Litinin yayin da yake kokarin bada kariya ga caji ofis din sabuwar unguwar da aka sake tsugunar da 'yan gudun hijira daga 'yan ta'addar da suka shigo cikin unguwar da kafa da tsakad dare.

Da yake tabbatar da mutuwar DPOn a yau Laraba, kakakin rundunar 'yan sanda jihar Borno, Nahun Kenneth, yace har yanzu rundunar na tattara bayanai akan harin.

Saidai, wani jami'in soja dake aiki a unguwar ta Sabuwar Marte ya shaidawa tashar talabijin ta Channels cewar 'yan taaddar na farautar wani mazaunin unguwar ne wanda ya tsere zuwa caji ofis din domin neman mafaka.

Jami'in sojan ya kara da cewar a kafa 'yan taaddar suka shiga unguwar sabanin babura da motocin da suka saba amfani dasu.

Unguwar Sabuwar Marte nada nisan kilomita 93 daga birnin Maiduguri a kusa da tafkin Chadi.

Unguwa ce da aka sake tsugunar da 'yan gudun hijirar da 'yan ta’addar suka daidaita a baya.

Har yanzu kungiyar ISWAP da abokiyar rigimarta Boko Haram na kaddamar da hare-haren bazata akan ayarin matafiya daga maboyarsu tare da birne nakiyoyi a gefen babbar hanyar.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG