Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Italiya Ta Ceto Bakin Haure 4,200


Wasu bakin haure da jami'an tsaron Italiya suka ceto

Har yanzu ana ci gaba da samun kwararar bakin haure daga kasashen marasa galihu zuwa sassan nahiyar turai, inda hukumomin tsaron Italiya suka bayyana ceto wasu mutane sama 4,200 a gabar tekun kasar.

Masu tsaron gabar Tekun kasar Italiya, sun ceto wasu bakin haure fiye da 4,200 a yankin Meditareniya.

Jami’an sun samu taimakon sojin ruwan kasar da na Jamus da kuma kasar Ireland, wadanda kasashe ne daga nahiyar Turai da suke gudanar da aikin hadin gwiwa daga Nahiyar Turai.

Sun kuma ce sun gano gawawwakin mutane goma sha bakwai, amma babu bayanai kan me ya haddasa mutuwarsu.

Sai dai jami’an Italiya na danganta irin wannan mutuwa da matsanancin halin gajiya da kishin ruwa da bakin hauren kaiya shiga, yayin da suke kokarin shiga nahiyar turai.

A ‘yan kwanakin nan an samu kwararar bakin hauren da dama, kuma masu sa ido a lamarin sun ce rashin doka da oda da kasar Libya ke fuskanta da matsanancin halin da yankin Afrika ta Arewa ke fuskanta, na daga cikin ababan da ke haddasa yin kaura.

Bidiyo

Shugaban Gwamnatin Rikon Kwarya A Mali Goita Ya Tsallake Rijiya Da Baya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Sanarwar Neman Afuwa daga Malam Abdujabbar Kabara
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:36 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Yi Tattaki Gida Bayan Ya Idar Da Sallar Eid El-Kabir a Daura
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:06 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Zauren VOA: Najeriya da Kaubalen 'Yan Aware - 005
please wait

No media source currently available

0:00 0:22:55 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Matsalar Tsangwamar Mata Masu Saka Abaya A Kanon Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG