Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ivan Duque Mai Ra'ayin Mazan Jiya Ya Lashe Zaben Shugaban Kasar Colombia


Ivan Duque sabon shugaban kasar Colombia
Ivan Duque sabon shugaban kasar Colombia

Ivan Duque mai ra'ayin mazan jiya ya doke Magajin Garin Bogota Gustavo Petro mai sassucin ra'ayi a zaben shugaban kasar Colombia tare da yin alkawarin mutunta yarjejeniyar 2016 da kasar ta cimma da kungiyar 'yan tawaye ta FARC

Dan majalisar dokoki mai ra’ayin mazan jiya, Ivan Duque, ya lashe zaben shugaban kasar Colombia da aka yi a kasar.

Duque ya yi alkawarin zai sabunta matsayar da aka cimma ta zaman lafiya a shekarar 2016 da kungiyar ‘yan tawaye ta FARC.

Ivan Duque, ya doke tsohon Magajin Garin Bogota, Gustavo Petro mai sassaucin ra’ayi da kashi 54 na kuri’un da aka kada, bayan zaben da aka sake a zagaye na biyu, yayin da shi Petro ya samu kashi 42.

Shi dai Petro ya kasance mai goyon bayan matsayar da aka cimma da kungiyar ‘yan tawaye ta FARC.

Sannan ya yi kyamfe dinsa ne akan cewa a sake raba filayen da ba a amfani da su ga manoma da ba su da karfi, a kuma karkata akalar kasar daga amfani da man fetur zuwa sababbin hanyoyin samar da wutar lantarki da ba su da illa ga muhalli.

Sai dai shi Duque da ya lashe zaben, ya yi alkawarin cewa, zai kara samar da yanayin da tattalin arzikin kasar zai bunkasa.

Ya na kuma so ya kawo sauyi a matsayar da aka cimma da kungiyar ‘yan tawayen FARC, inda ya nemi da a rika yankewa mambobin kungiyar hukuncin zaman gidan yari kafin a ba su damar shiga siyasa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG