Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ivory Coast Tana Gusawa Ga Sabon Yakin Basasa


Wuta tana ci lokacin arangama a tsakanin magoya bayan zababben shugaba Alassane Ouattara da dakaru masu biyayya ga Laurent Gbagbo, ranar 24 ga watan Fabrairu 2011 a Abidjan.
Wuta tana ci lokacin arangama a tsakanin magoya bayan zababben shugaba Alassane Ouattara da dakaru masu biyayya ga Laurent Gbagbo, ranar 24 ga watan Fabrairu 2011 a Abidjan.

'Yan tawaye sun ce sun kwace wasu garuruwa, yayin da aka roki magoya bayan Gbagbo su kai farmaki kan 'yan kasashen waje da sojojin Majalisar Dinkin Duniya a kasar

Kasar Ivory Coast tana kara gusawa ga sabon yakin basasa a bayan da ‘yan tawaye suka ayyana kama wasu sassan yammacin kasar, yayin da magoya bayan Laurent Gbagbo kuma suke kiran da a kai farmaki a kan ‘yan kasashen waje da sojojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya.

Shugaban matasa na jam’iyyar shugaba Laurent Gbagbo, Charles Ble Goude, ya ce ya kamata magoya baya su fatattaki baki daga unguwanninsu, yana mai fadin cewa lokaci yayi da wadanda ya kira “’yan Ivory Coast na asali” zasu mike domin kare kasar daga shisshigin kasashen waje da kuma sojojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya wadanda yace su na dafa ma ‘yan tawaye wajen yaki.

‘Yan tawaye sun ce sun kwace garuruwa biyu a kusa da bakin iyaka da Liberiya inda a da aka shata iyaka a tsakanin arewaci dake hannun ‘yan tawayen da kuma yankin dake hannun sojojin Mr. Gbagbo.

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon yace wannan fada da wanda aka yi a Yamoussoukro, rincabewar al’amura ce kuma tana gusar da kasar ga sabon yakin basasa. Shugaban ofishin kare hakkin bil Adama na Majalisar Dinkin Duniya a Afirka, Ibrahim Wani, ya fadawa VOA cewa akwai damuwa sosai game da daukar matasa sojojin haya da ake yi domin kara rura wutar fitinar Ivory Coast.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane akalla 315 aka kashe tun lokacin da aka bayyana sakamakon zaben Ivory Coast a farkon watan Disamba.

Akasarin kasashen duniya dai sun amince da Alassane Ouattara a zaman wanda ya lashe zaben shugaban kasa na watan Nuwamba, amma shugaba Laurent Gbagbo dake kan gadon mulki ya ki sauka yana mai ikirarin cewa shi ne ya lashe zaben.

XS
SM
MD
LG