Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iyalan Mutanen Da DSS Ke Tsare Da Su Na Neman Gwamnati Ta Yi Musu Adalci.


Hedikwatar Hukumar Tsaron Farin Kaya Ta Najeriya DSS

A yayin da hukumomin tsaro a Najeriya ke cigaba da tsare ‘yan kasuwan canji da gwal sakamakon zargin su da tallafawa ayyukan ta’adanci, yan uwa da abokan mutanen da ke tsaren na cigaba da kokawa kan rashin sanin halin da ‘yan uwan nasu ke ciki.

Batun cigaba da tsare wasu mutane sama da 400 da hukumomin tsaro a Najeriya ke yi na kara jawo kiraye-kirayen a bi tsarin da dokar kasa ta tanadar wajen hukunta wadanda ake zargi da aikata laifin tallafawa ‘yan ta’adda da ke addabar mutane musamman arewacin kasar.

Masanin sha’anin tsaro dakta Yahuza Ahmed Getso, ya ce cigaba da tsare mutanen da ake zargin ya sabawa doka, duba da yadda aka samu hujojji kan su.

Idan dai za a iya tunawa, daga karshen watan Februairu ne jami’an tsaro a Najeriya suka fara kamen ‘yan kasuwan canji bisa zargin su da tallafawa ayyukan ta’adanci.

Saurare cikakken rahoton a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:01 0:00

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG