Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iyayen Yara Makafi Na Tura Yaransu Bara Maimakon Makaranta A Nijar


Makarantar makafi dake birnin Konni na fama da matsalar rashin samun dalibai, domin iyayen yara na turasu bara maimakon makaranta.

Shekaru 16 da kafar makarantar ta makafi a birnin Konni dake jahar Tawa Jamhuriyar Nijar, amma yanzu dalibai mata da maza 11 ne kacal ke karatu a makarantar. Yayin da a tsawon shekarun yara 21 baki daya makarantar da karba.

A cewar shugaban makarantar mallam Nasiru Jibo, matsalar da ake fama da ita shine iyaye sun gwanmace su aika yaransu bara maimakon neman ilimi.

Shima daya daga cikin malaman makarantar wanda yake makaho, Boubacar Timogo, yace a kwai bukatar wayar da kan iyaye domin su gane muhimmancin ilimin ‘ya ‘yansu.

Iyayen yara makafi sun gwammace su aika su bara maimakon makaranta saboda rashin samun tallafi abin da ke kara yawan mabarata a kasar Jamhuriyar Nijar.

Domin karin bayani ga rahotan Harouna Mamane Bako daga Nijar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG