Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jakadan Belarus Ya Nuna Goyon Baya Ga Masu Zanga-zanga


Wasu masu manga zanga a birnin Minks na kasar Belarus da ke adawa da nasarar shugaba Alexander Lukashenko

Jakadan kasar Belarus a Slovakia, Igor Leshchenya, ya nuna goyon bayansa ga masu zanga zanga a wani faifain bidiyo da kafar yada labarai ta Nasha Niva ta Belarus ta wallafa a ranar Asabar, wanda ba a tantance ranar da aka nade shi ba.

A cikin bidiyon, an ga jakadan yana cewa “ina mai nuna goyon baya ga wadanda suka fito kan titunan biranen Belarus suke zanga zangar lumana domin su bayyana korafe-korafensu, ‘yan kasar Belarus sun sha wuya kafin su samu irin wannan dama.

Tun bayan da hukumomin zabe suka ayyana dadadden shugaban kasar da ake mai kallon mai mulkin kama karya, wato Alexander Lukashenko a matsayin wanda ya yi nasarar lashe zaben da aka yi a ranar 9 ga watan Agusta, ‘yan kasar ta Belarus suka fara zanga a birnin Minsk da sauran birane.

Sakamakon zaben ya nuna Lukashenko ya samu kashi 80 cikin 100 na kuri’un da aka kada yayin da babbar abokiyar hamayyarsa Sviatlana Tsikhanouskaya ta samu kashi 9.9 cikin 100.

‘Yar takarar ta kuma yi kira da a fita a yi tattakin “neman ‘yanci” a birnin Minsk a yau Lahadi.

Yayin da yake fuskantar wannn kalubale mafi girma tun bayan da ya hau karagar mulki, shugaban kasar ya yi wata ganawa ta wayar tarho da shugaba Vladimir Putin na Rasha inda ya nemi taimakon Moscow.

Shugaban ya ce al’amarin da ke faruwa a kasar ta Belarus ka iya zama babbar barazana ga Rasha ba Belarus kadai ba.

Fadar Kremlin a nata bangaren ta fada a wata sanarwa cewa, shugabannin biyu sun amince za a shawo kan “wannan matsala” ta Belarus “nan ba da jimawa ba” sannan kasashen biyu za su kara kyautata dangantakarsu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG