Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jakadun Amurka Da Na Chana Sun Yi Balaguro Zuwa Yankin Kasashen Koriya


Jakadun Amurka da na Chana sun yi balaguro zuwa zirin Korea, 'yan Kwanaki, bayan da Shugaba Trump ya kammala ziyarsa ta farko da ya kai a yankin.

Ziyarar ta mussaman ta jakdan China zuwa Korea ta arewa, wadda shugaba Trump, ya kira "babban mataki" ya kara tsamanin cewa watakila a sami mafita ta diplomasiyya.

Song Tao, manzo na mussamman ga shugaban Chana Xi (shi) Jinping, ya gana a Pyong-yang da manyan jami'an gwmnatin Korea ta arewa ranar asabar.

A cewar kafafen yada labarai na Korea ta arewa, wakilan sun yi musanyar ra’ayoyi akan batuttuwan da suka dami kasashen biyu a makurid koriyan, da kuma yankin baki daya, da kuma dangantaka tsakanin kasashen biyu.

Sai dai har yanzu jami'an Chana sun yi gum akan tafiyar, a taron 'yan jarida, wanda aka saba yi, a yau Litinin, ma'aikatar harkokin wajen kasar ta tabbatar da cewa har yanzu Song Tao yana Korea ta arewa, ba tare da wani karin bayani ba.

Wasu rahotanin sun bayyana cewa Tao Song zai gana da shugaban Korea ta arewa Kim Jong Un.

.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG