Accessibility links

Sabuwar Gwamnati A Afirka Ta Tsakiya Ta Bada Sommacin A Kama Tsohon Shugaban Kasar Francois Bozize, Kan Zargin Kisan Kai

  • Aliyu Imam

Michel Djotodia, shugaban 'yan tawaye da ya ayyana kansa shugaban kasa a jamhuriyar Afirka ta tsdakiya

Sabuwar gwamnati a jamahuriyar Afirka ta tsakiya ta bada sommaci na kasa da kasa a kamo mata tsohon shugaban kasar Francois Bozize, wanda aka hambarar da gwamnatinsa cikin watan Maris.

Sabuwar gwamnati a jamahuriyar Afirka ta tsakiya ta bada sommacin kasa da kasa na neman a kamo mata tsohon shugaban kasar Francois Bozize, mutuminda aka hambarar da gwamnatinsa cikin watan Maris.

Mai gabatar da kara na gwanatin kasar Alain Tolmo, yace ana tuhumar tsohon shugaban kasar da kisan kai, cin zarafin Bil-Adama, zuga mutane domin suyi kisan kare dangi, da laifuffuka da suka shafi tattalin arziki.

Tolmo yace an mika sommacin ga rundunar ‘yan sandana ta kasa da kasa watau interpol, ya kara da cewa ba da jumawa ba za’a tuhumi karin wasu mutane da ake zargi suna da hanu wajen aikata wasu laifuffuka.

Bozize ya tsere zuwa kamaru cikin watan Maris, bayanda mayakan kungiyar ‘yan tawaye da ake kira Seleka suka kai hari kan babban birnin kasar Bangui.

Kungiyoyin kare hakkin Bil’Adama sun zargi ‘yan tawayen da mummunar keta haddin Bil’Adama bayan sun juyin mulkin da suka yi.
XS
SM
MD
LG