Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Cuta Da Take Kama Makogoro Ta Kashe Karin Wasu Mutane Uku A Saudi Arebiya


Alamun kwayar cutar da kashe akalla mutane 30 a fadin duniya.
Hukumar kiwon lafiya ta duniya mai lakabin (WHO) a takaice, tace an sami karin mutane uku da suka mutu a kasar Saudiyya sakamakon kamuwa da cutan da ke kama makogoro ko hanyoyin iska da ake kira Coronavirus. Kawo yanzu cutar ta kashe mutane 30 a fadin duniya baki daya.

Wani kakakin hukumar ya fada jumma’a cewa jami’an kasar Saudiyyan ne suka tabbatarda mutuwar karin mutanen. Ya kara da cewa an sami sabon mutum daya da ya kamu da cutar cikin kasar a yankin da ake kira Al-Ahsa, wanda ya kawo jumlar wadanda cutar ta harba a fadin duniya baki daya ciki harda wadanda suka rasu, zuwa hamsin.

A bara aka gano cutar. Rabin wadanda larurar ta kama sun fito daga kasar ta Saudiyya.
Haka nan kuma an sami rahotannin cutar a kasashen da suke gabas ta tsakiya, da suka hada da Jordan da Qatar, da Tunisia, da kuma a turai.

A farkon makon nan wani mutum dan shekaru 65 da haifuwa a faransa ya mutu sakmakon kamuwa da cutar, shine mutum na farko da cutar ta halaka a kasar.

Kwayoyin cutar suna haddasa tari, da zazzabi da kuma pneumonia, kuma ana iya kamuwa da cutar idan aka kusanci wanda yake dauke da kwayoyinta sosai.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG