Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jamhuriyar Nijar: An Ba Da Umarnin Dage Dokar Ta-Baci A Yankin Tilabery


yanzu haka ofishin ministan cikin gidan Jamhuriyar Nijar ya bukaci gwamnan jihar Tilabery da ya janye dokar ta-baci da ya kafa a jihar.

Mako guda bayan da gwamnan yankin Tilabery ya bada sanarwar tsaurar matakin takaita zirga zirga a cikin binin Tilabery da nufin magance matsalar tsaro.

Jihar Tilabery tana daga cikin yankuna uku da hukumomin Jamhuriyar Nijar suka kafawa dokar ta baci da nufin magance matsalar tsaro da kasar take fuskanta, bayan da yan ta’adda suka kaddamar da hare hare.

Saboda yawan tsanantar wannan al’amari, gwamnan Tilabery ya bullo da wasu matakan hana zirga zirgar ababan hawa da masu tafiya a kafa daga karfe shida na yamma zuwa shida na safe.

Sai dai, ofishin ministan cikin gida na Jamhuriyar Nijar ya bukaci gwamnan jihar da ya janye dokar da ake ganin ta zarce ka’ida.

Yanzu haka mutanan yankin Tilabery sun fara bayyana farin cikin su da jin wannan sanarwa daga ofishin ministan cikin gida na kasar.

Ita dai gwamantin Jamhuriyar Nijar ta kafa wannan dokar ta baci ne a wadannan yankuna da izinin majalisar dokokin kasar.

Saurari cikakken rahoton Sule Mumini Barma daga Yamai:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:36 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG