Accessibility links

Jami’an Borno Sun Fusata da Gwamnatin Tarayyar Nigeria

  • Aliyu Mustapha

Gwamnan Borno Kashim Shettima

Manyan jami’an jihar Borno sun bayyana jin takaici da martanin da gwamnatin tarayya ta maido wa gwamnan Borno.

Wasu manyan ‘yan siyasa na jihar Borno sun kalubalanci jami’an gwamnatin tarayyar Nigeria da su fuskanci lalurorin dake gabansu maimakon musanta abinda shugabannin jihar Borno ke fada gameda tashin hankalin dake gallabar jihar. Wannan ya biyo ne bayan jayayyar da mai bada shawara ga shugaban kasa akan cudanya da jama’a, Doyin Okupe ya yi ne, inda yake musanta kalamin da gwamnan Borno Kashim Shettima yayi, yana cewa ‘yan Boko Haram sun fi sojojin Nigeria ingantattun makamai kuma sunfi su karfin gwiwar yaki, wanda Ukupe yace ba haka bane. Shi ne shi kuma a nashi murtanin, shugaban kwamitin watsa labarai na majalisar dokokin Borno yake gayawawakilin VOA Haruna Dauda Biu cewa idan gwamnatin tarayya ba zata taimaka wa Borno ba, akalla ta kyale jihar tayi fama da masifar da ta abka mata:

XS
SM
MD
LG