Jami’an KTT da na kasar Turkiya zasu gana yau Talata a birnin Brussels da nufin sake ci gaba da tattaunawa kan kokarin Turkiya na shiga kungiyar da aka shafe shekara da shekaru ana jan kafa a kai.
Dangantaka tsakanin Turkiya da KTT tayi rauni irin da ba a taba gani ba, biyo bayan yakin cacar baki tsakanin shugaban kasar Turkiya Recep Tayyup Erdogan da Brussels a kan kuri’ar raba gardamar da yasa aka kada dake cike da sarkakiya, da nufin kara wa’adin mulkinsa. Yunkurin sake kara dankon dangantakar ya biyo bayan ziyarar da Erdogan ya kai Brussels bayan nasarar da ya samu a kuri’ar raba gardamar da aka kada cikin watan Afrilu.
Facebook Forum