Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Tsaron Nijar Sun Ceto Danuwansu da Wasu 'Yanbindiga Suka Yi Garkuwa Dashi


Ministan Tsaron Cikin Gidan Nijar Bazoum Muhammadou daga dama da Abdulwahid Abdullahi Jibo a tsakiya da aka ceto sai kuma jami'in tsaro daga hagu

Ma'aikatar tsaron cikin gidan Nijar ita ce ta bada labarin ceto jami'in tsaro Abdulwahid Abdullahi Jibo bayan da ya kwashe watanni ukku a hannun mutanen da suka kai hari a sansanin jami'an tsaron Banibungu.

Lokacin da 'yanbindigan suka kai wa jami'an tsaron hari a Banibungu sun kashe jami'an tsaro biyu kana suka yi awan gaba da Jibo da kuma wani jami'in mai suna Habib Isa Gasibe a ranar 8 ga watan Nuwamban bara.

To saidai shi Habibu ya rasu a hannun maharan ranar da aka kamasu sakamakon mummunan rauni da ya ji.

Abdulwahid Jibo da iyalansa da ministan tsaron cikin gida
Abdulwahid Jibo da iyalansa da ministan tsaron cikin gida

Kawo yanzu gwamnati bata bayyana sunan kungiyar da tayi garkuwa da jami'an tsaron ba. Amma hukumomi sun ce sun cafke wasu da suke hada baki da maharan kwana daya bayan harin.

Jihar Tilaberi dake makwaftaka da kasar Mali ta fi kowace jiha fuskantar hare-hare a jamhuriyar Nijar bayan jihar Diffa wadda ta dandana kuda sosai sakamakon rikicin kungiyar Boko Haram.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:34 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG