Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami’ar Dutse Ta Kirkiro Dinya-Jari


Dinya
Dinya

Jami’ar tarayya dake Dutse a jihar Jigawa, ta yi wani yunkuri na kawo sauyi da farfado sana’ar alewar Dinya da Madi, inda aka koyar da mazauna ‘kauyen Rajun Dinya na karamar hukumar Dutse fasahar zamani ta sarrafa ganyen bishiyar dinya da ‘ya ‘yanta.

Bayan gudnar da bincike game da alfanun sanar sarrafa ‘ya ‘yan bishiyar Dinya da ganyen ta wadda aka kwashe shekaru aru-aru anayi a kasar Hausa, wadda kuma a ‘yan shekarun nan ta kama tafarkin durkushewa. Hukumomin Jami’ar tarayyar dake Dutse sun bullo da tsari na musamman ga mata da matasa na ‘kauyen Rajun Dinya kan sabuwar fasahar farfado da wannan sana’a mai tarihi.

Malama Ramatu Yahaya, dake zama daya daga cikin matan dake sana’ar Madi da Alewar Dinya a ‘kauyen Raju, ta bayyanawa Muryar Amurka yadda suke samowa tare da sarrafa Dinya.

Ganyen Dinya
Ganyen Dinya

Farfesa Fatima Batul Umar dake zaman shugabar jami’ar tarayya ta Dutse ta fayyace dalilin bullo da sabuwar fasahar. Inda ta ce sun bullo da wannan shiri ne domin al’ummar dake yankin su amfana

Malam Mati Garba shugaban matasan da suka koyi sabuwar fasahar cewa ya yi wannan ilimi da suka samu ya taimaka musu sosai da sosai, saboda sun fahimci cewa a baya basu san yadda ake sarrafa Dinyar ba.

Mataimakin gwamnan Jigawa Barrister yace zasu tallafawa wannan yunkuri na Jami’ar tarayya ta Dutse na habaka tattalin arzikin iyali.

Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Mahmud Ibrahim Kwari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG